Ali Al-Ashiri babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar a jiya Alhamis ya bayyana cewa; Dole ne Misrawa mazauna kasar Libiya su dauki matakan kula da taka- tsantsan kuma su kauracewa yankunan da ake gumurzu tsakanin kungiyoyin da suke dauke da makamai a kasar ta Libiya. Sannan ya gargadi direbobin dogayen motoci ‘yan Masar da suke shiga cikin kasar Libiya ta mashigar Salum da su guji bin garin Tabruq da ke arewa maso gabashin kasar ta Libiya.
Har ila yau Al-Ashiri ya bukaci ma’aikatan karamin ofishin jakadancin Masar da suke Libiya da su fice daga kasar ta hanyar mashigar Ra’as Jadir da ke tsakanin kasar Libiya da Tunusiya, sannan ya kara jaddada yin kira ga dubban ‘yan kasar Masar mazauna Libiya da su hanzarta dawowa gida sakamakon tashe-tashen hankula da suka yi kamari a kasar ta Libiya. ABNA